MATSAYIN MACE A TARBIYYA TA SUFANCI: DARASI DAGA RAYUWAR NANA ASMA’U ƊIYAR SHAYHU USMANU ƊANFODUYE
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMAH MAI JIN KAYI
TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU TABBATA GA ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAYHI WA
SALLAM
Addinin Musulunci ya zo da tsarin da ya ba wa mace matsayi na daraja a
cikin iyali, al’umma da kuma fagen ilimi. Tarihin Musulunci ya nuna
cewa mace ba kawai mai tarbiyyar gida ba ce, har ma ginshiƙin al’umma
ce. A ƙasar Hausa kuma, mace ta kan taka muhimmiyar rawa a fannoni
da dama, musamman wajen ilimi, sufanci da al’adu na zamantakewa.
Wannan makala za ta yi nazari kan matsayin mace a tarbiyya ta sufanci
ta hanyar duba rayuwar fitacciyar Malama kuma marubuciya, Nana
Asma’u Ɗiyar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, sannan ta kawo darussa da
shawarwari ga iyaye da mata da har a yau ana cin gajiyasu.
Ma’anar Mace
A Lugga (Linguistically): Mace ita ce jinsin ɗan Adam wanda ya
bambanta da namiji ta siffofi da dabi’u na halitta.
A Istilahi (Terminologically): Musamman a mahanga na shari’ar
Musulunci, mace ita ce wacce take rabin al’umma, mai ɗaukar nauyin
tarbiyya da samar da ci gaban iyali, wacce kuma take da hakki da nauyi
bisa koyarwar Alƙur’ani da Sunnah, wanda a tarbiyyar sufanci ake
kimanta matsayinta wurin kebacewa da kulawa da soyayya a dukkan
matakai.
Files
What's Your Reaction?