GUDUN MAWAR MALAMAN SUFANCI WAJEN HABAKA KIMIYYA DA FASAHA
TARON NATIONAL QADIRYYA MEDIA
CONNECT 2025
GUDUN MAWAR MALAMAN SUFANCI
WAJEN HABAKA KIMIYYA DA FASAHA
MAI GABATARWA
ALIYU GARBA
07/09/2025
MBY EVENT CENTRE UNGUWAR JAMBULO 3
RD GATE
OPPOSITE AA RANO JAHAR KANO AREWA MASO
YAMMACIN NIGERIA
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI, TSIRA DA AMINCI
ALLAH SU KARA TABBATA GA FIYYAYYEN HALITTAH ANNABI
MUHAMMAD (S.A.W), DA YAN GIDANSA DA SAHABBAN SA DA
WADANDA SUKA BIYO BAYANSU BISA TAFARKIN SA.
JINJINA DA SALLAMA TA MUSAMMAN GA SHUGABAN DARIKAR
QADIRIYYA TA AFRICA GABA DAYA, JAGORANMU ZUWA GA
TAFARKIN GASKIYA MAULANMU, HALIFA SHEIKH QARIBULLAH
MALAM NASIR KABARA.
Sallama irin ta Addinin Musulunci ga manyan baki, da wandanda suka halarto
wannan taro mai Albarka na National Qadiriyya Media Connect 2025, da kuma
wadanda suka shirya wannan taro, ina cewa Assalamu Alaikum Warahamatullahi
Ta`ala Wabara katuhu.
Na Tsaya a wannan wuri ne badan nakai ba, ba dan na isa ba, ba dan wani cikakken
ilimi danake takama dashi ba, sai don soyayya da nakema malaman sufaye da hasken
su danake gani dashi, domin in danyi yar karamar Makala mai taken ``Gudummuwar
malaman Sufanci wajen Habaka Kimiyya da Fasaha``.
Inason mu sani Makala akan malaman sufaye da al`amarinsu Yasha bam-bam da duk
wata Makala da za`a gabatar wadda ba tasu ba, saboda bayani akansu yafi tasiri a
zuciyar Al-ummah fiye da rubutu a takarda game dasu.
Wannan Makala tsakure zanyi a rubutu, sa`annan inyi bayani da fadi daga bakina.
Ina rokon allah yaimin gudunmuwa.
SASHIN FARKO
Mahangar malaman kimiyya da fasaha na zamani gameda da dan adam da kuma
abinda ya kaisu ga bincike cewan lallai ilimin nasu daga addini ya fito ta hannun
malaman Addinin.
1. ALBERT EINSTEIN (1879-1955) mutumin kasar jamus wanda akeji dashi
a duniyar kimiyya da fasaha, yake cewa abinda malaman Addini suke fadin
suna Ji {YANAYI} shine ya bamu karfin zuwa ga bincike akan kimiyyah da
fasaha yake cewa, Sa-annan dashi da Almajiransa sun fadama daliban ‘daya
daga cikin malaman kimiyya da fasaha na duniya wato ISAAC Newton
(1845-1727) cewa dan Adam da kuke gani ya wuce yadda kuka ‘daukeshi,
yana da bangarori daku ba kula dasu ba, kunfi kula da gangar jikinsa ne kawai
da abinda jikin ke iwatar wa (BAYANI DA BAKI).
2. A sama sun ambaci addinai irinsu addinin Hindu, Buddha, Kabbala da
addinin Kiristanci, da kuma addinin Muslunci (wanda shine kadai wanda yake
da mabudin ilimin kimiyya Da fasaha na asali). A tambaya anan ya akayi suka
gano suka kuma fahimci cewa duk sauran addinan basu bada haske ko
mallakan mubudin ilimin kimiyya da fasaha?
Amsar itace sunyi bincike mai zurfi akan dan Adam ta bangaren Qur`ani,
Hadisi da Manzan Allah (S.A.W). Ga yadda binciken su ya Gudana.
- Da farko sun kalli ayar datai Magana akan yadda Allah (S.W.A) ya halicci
dan Adam Acikin `suratul Hijrih aya ta 28-29
“kuma a lokacin da ubangijinka ya cewa mala`iku, lallai ni, mai Halittar
wani jikine daga kekasashshiyar yun’bu wanda ya canza.
- To idan na daidata shi kuma na Hura Ruhina a cikinsa, to ku fadi a gareshi
kuna masu yin sujjada.
- Ayoyi guda biyun na sama sunsa wandannan malaman kimiyya sunyi
bincike akan dalilin hura wannan ruhin a jikin dan Adam?
AMSA
- Saboda wata Daraja daya kebe ma dan Adam.
- Saboda ya samu kusanci da wata soyayya naya bauta masa bautan hakika.
- Dan ya sami wani sashe na ilimi daga Allah madaukakin sarki wanda
baibawa wata halitta ba.
Wadannan malaman kimiyya da fasaha sun kara bincike akan ta wadanne
hanyoyi dan Adam zai samu wannan gatan?
SAKAMAKON BINCIKE:
1. Ta aiko Annabawa -har zuwa annabin karshe.
2. Salihan bayi magada Annabawa.
Wadannan masu bincike sunyi bincike akan wannan annabi daya zo da Al-Qur`ani;
Manzan Allah (S.A.W) akan banbancinsa da sauran annabawa.
SAKAMAKON BINCIKEN MAI ZURFI
1. Haskensa aka fara halitta Kafin a halicci komai
2. An bude ofishin annabta da hasken sa.
3. Shine ya bayyana a karke
Suratul Ahzab aya ta 21 ta kara musu haske
Lallai abin koyi mai kyau ya kasance gareku daga manzan allah ga wanda ya
kasance yana fatan rahmar Allah, da ranar lahira kuma ya ambaci Allah da yawa.
4. Yadda ya rayu daga haihuwarsa, tasowan shi, al`amuran daya tashi a cikinsu,
zuwan shekaru 40 kafin annabta.
5. yadda aka wanke zuciyarsa.
6. Ilminsa na yadda ake ma rai tarbiya, da wankin zuciya da kuma yadda yake
bautar Allah da kankar dakai.
Wandannan masu binciken, sun kara matsawa gaba sun binciko ofisoshin da
manzan Allah ya rike kamar haka!!
- Ofishin saukar da wahayi
- Ofishin fassara Ayoyin da aka saukar
- Ofishin gudanarwa na gwamnati da kuma.
- Ofishin tarbiyyar rai, da wankin zuciya.
- Sun fahimci cewa bayaan wafatin manzon Allah (S.A.W), Ofishin wahayi
ya daina aiki.
- Ofishin fassara ayoyi yaci gaba (Malaman Tafsiri)
- Ofishin gudanar da gwamnati (Halifanaci yaci gaba tun daga sayyidina
Abubakar) (R.A).
- Ofishin tarbiyar rai da wankin zuciya, ya cigaba.
- Masu binciken sunyi dogon Nazari akan wannan ofishin na tarbiyyan rai
da wankin zuciya sun binciko abubuwa kamar haka;
1. Matsayin rai a rayuwar dan Adam a duniyar Musulunci daga ayoyin
Qur`ani da Hadisan ma`aiki (S.A.W). s
2. Matsayin zuciya a rayuwar dan adam a duniyar musulunci daga al`qurani da
hadisan shugaba (SAW).
A gameda ayar data shafi tarbiyyar rai;
i. Suratul yusuf aya ta (25)
ii. Suratul Ahzab aya ta (22)
iii. Jihadin Nafsi (Hadisi).
A gameda da tsarkake Rai: -
Suratul Shams
3. Binciko tsarkake rai da Allah subhanahu wata ala yake da kansa, shuqaba (S.A.W)
yakeyi, da kuma shi kansa mutum damar duya samu don yin wannan aiki
Tsarkakwar Da Allah Keyi;
i. Suratul Nisa’I (49)
ii. Suratul Nur (21)
Tsarkakewan Da Manzan Allah Keyi
Suratul Ali Imran (164)
Shugaba (SAW) aiki uku yake a wannan ayar;
1. Ya nuna ma mutane ayoyin Allah.
2. Yana Tsarkakesu (Tazkiyya).
3. Yana kuma koyar dasu littafi da Hikima bayan Tazkiyya.
A wannan aya wadannan masu bincike sun gano ma`anar hadisin dayake Magana
akan cewa shugaba (S.A.W) yace hikima wani abune daya bacema mumini, duk
inda yagansa, ya dauki abinsa.
Tsarkakewan Da Mutum Kema Kansa
i. Suratul A`Ala (14 - 15)
ii. Suratul Shams (8)
4. Binciko yadda qur`ani da hadisi sukayi bayani akan zuciya;
Zuciyar Data Kulle Matacciya
i. Suratul Baqara ayata (17 - 18).
ii. Suratul Muhammad ayata (12).
Zuciya Mai Dauke Da Cutittika Kuma Kekasashshiya
i. Baqara (10)
ii. Baqara (74)
iii. Zumar (79)
Hadisin Bukhari akan wata tsoka a jikin dan Adam wanda shugaba (S.A.W) yai
bayani.
5. Binciko yadda Qur`ani yayi bayani akan rai da tsarin tarbiyyarsa da abinda
ke biyo baya kamar Haka;
Nafs Ammara – Suratul Yusuf (52)
Nafs Lawwama _ Suratul Qiyama (2)
Nafs Nafs Mulhama – Suratul Shams (7 - 8)
Nafs Mutma – Innah –
Suratul Fajir (2)
Suratul A`Araf (124 - 126)
Suratul Tauba (40)
Nafs Radiya – suratul Fajr (28)
Nafs Mardiyu - suratul Fajr (28)
Suratul Bayyinat (8)
Nafs Kamila –
6. Binciko yadda zuciya take komawa bayan tarbiyyar rai da wankin ta
Sakamakon bincike shine, Cikan burin da aka busama dan adam ruhi saboda
su, wa’inda na lissafa guda uku a farkon wannan Makala.
A nan masu wannan bincike, sun binkici mabudin wadannan ayyuka dana ambata a
baya na tarbiyar rai da kuma wanki ko tsarkake zuciya, cewa menene mabudin
wannan aiki? Da abin da zai biyo baya? Sakamakon bincike SHINE: - ZIKIRIN
ALLAH madaukakin sarki kamar yadda wa`dannan ayoyi suka tabbatar musu.
Suratul Ahzab (41)
Suratul Muzzammil (8)
Suratul Nurr (37 - 38)
Suratul shu`ara`i (86 - 87)
Suratul Qaf (31 - 33)
Suratul Ra`ad (28)
Suratul baqara (150)
Suratul baqara (151)
Suratul baqara (152)
Suratul A`araf (205 - 206)
Suratul Hiijri (39 - 45)
Suratul Yunus (62)
7. masu wannan bincike na kimiyya da fasaha, sun binciki cewa su wannene suka
tare a wannan ofishi na tarbiya, Suke wannan zikiri da kuma irin wannan irin
sakamako da zasu samu daga Allah madaukakin sarki?
SAKAMAKON BINCIKE: shine wadannan bayin Allah sune sufaye masu
Ambaton Allah safe da maraice, wadanda suka tare akan zuciya da rai.
Nanne ma`aikatarsu, nan ne ofishin su.
Wadannan masu neman ilimi akan rai da zuciya, sune:
• Ma`abuta rai da zuciya
• Sahabban rai da zuciya
• Masana ilimin rai da zuciya
• Wa`inda suka amsa kira da karfi suka sallama, sallamawa a lokacin da
sukaji kiran Allah Subhanahu wa ta`ala
Suratul Anfali (24) BAYANI DA BAKI.
SASHI NA BIYU
Anan masu bincike gameda yadda musulinci ya bada gudummuwa akan ilimin
kimiyya da fasaha ta hannu malamai sufaye, sun kara nutsuwa bincike mai zurfi
wajen gano abubuwan dake wanzuwa lokacin da suka nutsa cikin zikiri akan rai da
zuciya. kafin na ambaci abubuwan da suka gano inaso in Ambato mutane biyu
wadan da suba malaman kimiyyah da fasaha bane amma sunyi zurfi wajen bincike
game da sufaye da lamuransu;
A kwai farfesa Reynold alleyne Nicholson, dan kasar England (1945), Da kuma
farfesa Willium Clark Chittick, na kasar Amurca (1943). Wadannan bayin Allah
sun kara nunama malaman da suka yi kokari akan sanin ilimin kimiyyah da fasaha
hasken sufaye da sirrin da suka tara akan wannan fanni.
Ga Abubuwan da suka gano cewa yaki na tashi tsakanin mai zikiri da kuma
wadansu abu uku da suke tare masa hanya wajen kaiwa ga Allah madaukakin sarki,
wanda Maulana Najmuddeen kubra (Hijra 540 - 618) yai bayaninsu kamar haka:
kana fara yin zikirin Allah, Ya fara zama a jikinka, to wani haske zai taso don ya
kori duhun dake cikin zuciyar mai zikiri, abinda hasken zai fara nuna masa shine
abubuwan da suka tare masa hanya a tafiyar sa ta neman ilimin Allah madaukakin
sarki, wadanda gasu kamar haka;
1. Yanayin halittarsa (Ruwa, Kasa, Iska da kuma yanayin bangaran Wuta).
2. Nafsi Ammara.
3. Shaitan.
Malam majmuddeen kubra yace zikiri zaiba mai yinsa dama ya samu
galaba akansu ta hanyar haske da zai bayyana a cikin zuciyar mai yi
(BAYANI DA BAKI).
Masu bincike sun kara nutsawa tekun bincike akan danganta tsakanin zikiri da
Numfashi inda suka binciko al`amura kamar haka:
(BAYANI DA BAKI)
SASHI NA UKU
Bincike akan yanda annabawa da wasu bayin allah suke sarrafa numfashinsu mai
karfi ta hanyar zikiri wajen bayyana mu`ujiza da karamoni, da duk wasu al`amura
da suka zarce tunanin dan Adam.
Suratul Baqara (253)
Suratul Ali`Imran (47)
Suratul Anbiya (83 - 84)
Suratul Sad (41 - 42)
Suratul Namli (40)
Hadisin sahabin daya warkar da wanda kunama ta harba.
Hadisin bawan Allah/ sahabin daya tashi jaki.
Karamar SHEHU AHMADU BAMBA da yai sallah akan ruwa
Karamar maulanmu SHEHU ABDULQADIR JILANI quddisa – sirrahu akan
1. Shan magani
2. Kan waken da maulana malam kabara yai masa
BINCIKE: Akan bambamcin malaman sufaye masana Allah da bokaye
(BAYANI DA BAKI)
Rufewa
❖ Imamul Gharzali Akan Harkar Neman Ilimi
❖ Maulana Abu Qasim Alqushairih akan shawara daya ba muridai.
❖ Suratul Baqara (257)
Wassalam Alaikum Warahmatullahi Ta`ala wa barakatuhu
ALIYU GARBA.
Files
What's Your Reaction?